Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta mika zunzurutun kudi har kimanin sama da naira bilyan daya ga Hukumar Alhazai ta kasa NAHACO, a matsayin kudaden kujerun Hajjin da Hukumar ta amince su gudanar da aikin Hajjin bana a jihar daga jihar. Babban Sakataren Hukumar na jihar, Alhaji Muhammad Sani Ahmad ne ya sanar da haka a yayin tattaunawarsa da manema labarai cikin makon da ya gabata a Dutse.
Sakataren ya kuma bayyana cewa, kimanin kujeru 2,300 ne aka baiwa jihar jigawa, wadanda tuni maniyyatan suka biya kudadensu dari bisa dari. Ya kara da cewa, Hukumar aikin Hajji ta jihar, tuni ta kammala duk wasu shirye-shirye domin tunkarar aikin na wannan shekara ta 2015.
Malam Sani ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar, karkashin jagorancin, Alhaji Muhammad Badaru ta samar da wadatattun gidaje a birnin Makkah domin maniyyatan jihar. Daga nan ya yi kira ga maniyyatan da suka fito daga jihar su kasance wakilan jihar nagari a yayin gudanar da aikin Hajjin domin kare kimar jihar, Jigawa da ma kasa baki daya.
A wata sabuwa kuma, Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya mika sakon ta’aziyyarsa ga takwaransa na jihar Borno, tare da daukacin al ‘ummar jiha Borno bisa rasuwar Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Zanna Mustapha, wadda ya rasu a daren Asabar din makon da ya gabata. Wannan sakon ta’aziyya na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke das a hannun mai taimaka wa Gwamnan kan harkokin yada labarai, Malam Bello Zaki.
Takardar ta ci gaba da zayyana cewa Gwamnan ya kuma jajanta wa iyalin Mataimakin Gwamnanda sauran al’ummar jihar baki daya. Inda Gwamna Badaru ya bayyana rasuwar mataimakin Gwamnan a matsayin wani babban rashi, ba a jihar Borno kadai ba, har ma da kasa baki daya.
Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Title :
Jigawa Ta Mika Bilyan Guda Ga Hukumar Alhazai Ta Kasa
Description : Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta mika zunzurutun kudi har kimanin sama da naira bilyan daya ga Hukumar Alhazai ta kasa N...
Rating :
5