Assalamu alaikum Malam. Wani Majinyaci ne yana cikin rashin lafiyarsa sai matansa sukayi masa laifi. Suna hayaniya da junansu. yace musu su dena amma sukayi banza dashi. Shi kuma saboda bacin rai sai yace musu "Kowacce ta tafi gidansu na sakeku".
Bayan yayi wannan sakin da wata biyu sai Allah yayi masa rssuwa. Abinda muke tambaya ana shine: Shin wadannan matan zasu ci gadon dukiyarsa, ko kuwa ba zasu samu ba??
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Malamai sunyi sabani akan wannan mas'alar. Amma dai maganar Imamu Maliku (rah) ita ce In dai Majinyacin ya rasu ne acikin wannan jinyar da yake yi, Kuma saki daya yayi musu ko biyu, Kuma har zuwa lokacin rasuwar tasa matan basu gama Iddah ba, to za'a raba gado dasu. Zasu ci gadonsa..
WALLAHU A'ALAM.