Kalmomi ne jerarru cike da hikimomi da wa'azozi, kumq sun fito daga bakin wanda ba ya fada son rai. Ba ya magana sai da wahayi daga Rabbul Izzati.
Ga kadan daga ciki:
1. Manzon Allah (saww) yace: "MUTUM HUDU, HAKKI NE AKAN ALLAH CEWA BA ZAI SHIGAR DASU ALJANNAH BA, KUMA BA ZAI DANDANA MUSU NI'IMOMINTA BA :
- MAI KWANKWADAR GIYA.
- MAI CIN RIBAA (KUDIN RUWA - INTEREST).
- MAI CIN DUKIYAR MARAYA BA TARE DA HAKKI BA.
- MAI BIJIRE MA IYAYENSA.
(Imamul Hakim ne ya ruwaito hadisin acikin Mustadrak).
Wannan hadisin gargadi ne zuwa ga dukkan Musulmi. Idan an ce MAI KWANKWADAR GIYA, ana nufin har masu shan kwaya, da masu shan Weewi, da sauran kayan maye. Domin duk abinda ke bugarwa shima giya ne.
MAI CIN RIBAA - Wannan gargadi ne ga masu hulda da bankuna, da masu hulda da kampanonin Inshaura (Insurance companies) da masu huldar kasuwanci da Ma'aikatan Gwamnati. Sai a kiyaye domin shi Allah ba ya mantuwa. kuma yana nan a madatsa zaka je ka iskeshi, Kuma zaka karbi sakamakon ayyukanka aranar da Nadama ko istigfari ba zasuyi amfani ba.
CIN DUKIYAR MARAYA BA TARE DA HAKKI BA :Wannan yana daga ciki. zunubai mafiya girma, masu saurin hallakarwa kamar yadda yazo acikin wasu hadisan masu yawa.
Kuma duk wanda yaci dukiyar marayu da zalunci, to hakika wuta yake ci acikin cikinsa. Kuma daga ranar da ya mutu wutar zata fara balbaleshi acikin Qabarinsa. Aranar Alkiyamah kuma za'a ganshi wutar tana fitowa ta bakinsa.
Wannan gargadi ne ga masu aiki a hukumar fansho. Wadanda suke wawurar kudin marayu da niyyar cin hanci. Tsinuwar ta zama biyu kenan. ga tsinuwar cin hanci, ga kuma tsinuwar cin kudin marayu.
Kuma gargadi ne ga 'Yan uwan Uban marayu. (wato Kawunnai, baffanu da sauransu) wadanda ake basu ajiyar dukiyar marayu.
BIJIRE MA IYAYE: Mafiya yawan matasan zamanin nan, ko abokinsu yafi iyayensu mutunci awajensu. Suna ganin mahaifansu kamar wasu Qazamai, Mushrikai, 'Yan kauye, etc. Don haka idan sun fadi magana bazasu dauka ba. Kuma basu da mutunci agunsu.
DAGA ZAUREN FIQHU.