Ma'aiki (alaihis salam) yace:
ABUBUWA GUDA HUDU BASSU KOSHI DA ABUBUWA HUDU:
- Qasa batta koshi da ruwa.
- Mace batta Koshi da namiji.
- Idanuwa bassu Koshi da kallo.
- Malami ba ya Koshi da ilimi.
(Imamul Hakim ne ya ruwaito).
*******************************
2. MUTANEN NAN GUDA HUDU ALLAH YANA FUSHI DASU:
- Dan kasuwa mai yawan rantsuwa.
- Matalauci mai girman kai.
- Tsohon Mazinaci.
- Azzalumin shugaba.
(Imamun Nisa'iy ne ya ruwaito hadisin).
**********************
3. ABUBUWA GUDA HUDU SUNA DAGA CIKIN DACEWAR MUTUM :
- Matarsa ta kasance Saliha (mace tagari).
- 'ya'yansa su kasance masu biyayya.
- Abokan huldarsa su zamanto Salihai.
- Arzikinsa ya kasance a garinsa.
(Dailamiy ne ya ruwaito daga Aliyu bn Abi Talib r. a.)