1. Annabi (Saww) yace : ''Duk wanda ya Gina
ma Allah Masallaci,
to Allah zai gina masa gida a cikin
Aljannah.
(Bukhari da kuma, Tirmidhi hadisi
na 318)
2. Annabi (Saww) Yace : ''Wanda yayi Salloli
biyu na sanyi (Sallar La'asar da Sallar Asuba)
zai shiga Aljannah.'' (Bukhari)
3. An kar6o Hadisi daga Abu Hurairah (RA)
yace : Annabi (Saww) Yace : ''Duk wanda yace :
''SUBHANALLAHI WABIHAMDIHI,
SUBHANALLAHIL-AZEEM.'' Sau bakwai (7)
za'a gina masa bene a cikin Aljannah.
''Al-wabilus Sayyib Shafi na 77.''
4. Jabir, Allah ya yarda dashi, yace:Annabi
(Saww) Yace : ''Wanda yace : ''SUBHANALLAHIL
-AZEEM WABIHAMDIHI.'' za'a dasa masa
bishiyar Dabino a cikin Aljannah.''
5. Annabi (Saww) Yace : ''Duk ! Wanda Qarshen
Maganarsa ta kasance ''LA'ILAHA ILLALLAH.''
zai shiga Aljannah.'' (Abu Dawud)
6. Annabi (Saww) Yace : ''Duk ! wanda Yace :
''Ya Allah Ina Rokonka, ka Shigar dani Aljannah
sau ukku (3) (Allahumma Inniy As'alukal
jannah) ALJANNAH ZA TA CE : ''Ya Allah ka
shigar dashi Aljannah.''
(Tirmiziy ne ya ruwaita shi)
7. Annabi (Saww) Yace : ''Ya ku ! Mutane ku
watsa Sallama, kuma ku ciyarda da Abinci ga
mai jin yunwa, kuma kuyi Sallah lokacinda
Mutane ke bacci (da dare) sai ku shiga Aljannah
da Aminci.''
(Tirmiziy ne ya ruwaito shi)
8. Manzon Allah (Saww) Yace : ''Lallai Allah
yanada sunaye Tis'in da tara (99), Duk ! wanda
yasan Ma'anar su kuma ya kiyayesu Zai shiga
Aljannah.'' (Bukhari)
9. Annabi (Saww) Yace : ''Wa zai Lamunce min
Abinda ke tsakanin Ha6o6insa guda biyu da
kuma Abinda ke tsakanin kafafunsa biyu (Wato :
Harshen sa da kuma Farjinsa) In Lamunce masa
Shiga Aljannah.''
( Sahih Bukhari )
10. An kar6o Hadisi daga Aisha (RAH) tace :
Annabi (Saww) Yace : ''Duk ! wanda ya ga wata
kafa
a cikin Sahu kuma ya toshe, Allah zai gina Masa
gida a cikin Aljannah kuma zai daukaka
darajarsa a cikin Aljanna.''
Allah yasa mu dace.