Assalamu alaikum.
Malam, ina yi maka fatan alheri. Allah ya saka maka da aljanna a bisa 'ko'karin da kake yi na ilmantar da al'umma.
Shin za a iya sanyawa ko radawa yaro suna MUHAMMADIL-HADI? Ko kuwa ABDULHADI ake nufi? Na gode daga Rabiu Barau.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Muna godiya sosai abisa addu'o'in alkhairi da muke samu kullum daga gareku. Allah ya saka muku da alkhairi.
Eh ya halatta ka sanya ma yaronka suna MUHAMMADUL HADI ko kuma ka sanya masa ABUDUL HADI...
Dalili anan shine: Allah da kansa ya kira Manzonsa da sunan ALHADI (wato mai shiryarwa) acikin Suratush Shura, ayah ta 49. Yace masa "HAKIKA KAI KANA SHIRYARWA ZUWA GA HANYA MADAIDAICIYA".
Kuma ya kira kansa da suna "ALHADIY" a gurare masu yawa Acikin Alqur'ani Mai Girma. Misali kamar inda yake cewa: "HAKIKA ALLAH YANA SHIRYAR DA WANDA YASO ZUWA GA TAFARKI MADAIDAICI".
Wadannan sunayen duk suna da kyau. Manzon Allah (saww) yana cewa: "FIYAYYEN SUNAYE, SHINE WANDA AKA HADA DA "ABDUL" KO KUMA WANDA AKA HADA DA "HAMDU" (WATO KAMAR AHMADU KO MUHAMMADU, KO HAAMIDU, KO MAHMUDU)..
WALLAHU A'ALAM.