Assalamu alaikum. Malam shekaranjiya a masallacin hostel dinmu wani malami ya sake cewa wai babu kyau mutum yayi azumin nafila batareda yayi ramuwar na farilla ba. A cewarsa wancan hadith ba dalili ne da zaisa ayi hakan ba, saboda ta Iya yiwuwa Nana Aisha R.A ba lallai ne tanayin sittu Shawwal dinba tunda ba farilla ne ba.
Kuma yace yin azumin sittu Shawwal batare da biyan Ramadan ba bayada wani lada. Shine ni abin ya confusing dina nake son dan Allah Malam ayi min bayani cikakke, shin dagaske ne babu lada idan mutum yayi azumin nafila bai rama Ramadan ba? Kuma dagaske ne akwai yiwuwar cewar Nana Aisha R.A batayin azumin sittu Shawwal? Dan Allah ina Neman Karin bayanin abinda ya dace. Wassalam alaikum.
AMSA
*******
Wa alaikis salam Wa rahmatullah wa barakatuh.
Hakika wannan Malamin ya gina fatawar tasa bisa zato da kuna rashin tabbas, da rashin Hujjah.
- Da farko yace wai zata yiwu Sayyida Aisha bata yin azumin Sittu Shawwal din. Alhali wannan zaton nasa ba haka bane.
Ga abinda bincikena ya tabbatar min nan: Urwatu bn Zubair (Almajirin Sayyidah Aisha ne, kuma 'dan yayarta ne-(ra) yace: "A'ISHA TA KASANCE TANA BIBIYAR AZUMI (WATO TANA YINSA WANI BAYAN WANI BATTA HUTAWA).
ALQASIM (Shima Almajirinta ne) yace: "A'ISHA TA KASANCE TANA YIN AZUMIN SHEKARA NE. BATA AJIYE AZUMI SAI RANAR SALLAR BUDA BAKI, KO KUMA SALLAR LAYYA".
Aduba cikin SIFATUS SAFWAH na Ibnul Jawzee juzu'i na 2 shafi na 15. da kuma TABAQAT ALKUBRA na Ibnu Sa'ad juzu'i na 8 shafi na 37.
Kuma an ruwaito daga gareta cewa takan bar ramukon azuminta wani lokacin har sai acikin watan SHA'ABAN yakeyi. Kum wannan bai hanata yin duk wani azumin nafilah ba. Don haka maganar wancan malamin ba daidai bane.
Ya kamata ya kyautata mata zato amatsayinta na wacce tafi kowa sanin yadda Mijinta (saww) yake yawaita tsaiwar dare, Azumin nafila ko yaushe, etc.
Amatsayinta na wacce taga Qafafaun Mijin nata sun kumbura saboda Qiyamullaili, sai tace masa ya rika hutawa mana. tunda Ubangiji ya riga ya gafarta masa. Sai Yace mata "SHIN BA ZAN ZAMA BAWA MAI GODIYA BA! "
2. Maganarsa kuma ta biyu da yace wai babu lada ga duk wanda ya azumci SITTU SHAWWAL ba tare da ya gana ranuko ba, shima wannan zance ne marar tushe. Hakanan cewarsa da yayi wai babu kyau ayi hakan, shima bashi da Hujjah.
Shi dai lada awajen Allah yake. Kuma shi kadai ke bayarwa. Kuma babu wata ayah ko hadisi wanda yazi da wannan bayanin da malamin nan yayi.
Duk wani abu ba ya zama haramun sai in ayar Alqur'ani ce ta haramtashi, ko kuma Sahihin hadisin Manzon Allah (saww).
Kamar yadda muka fada awancan karon, an fi son mutum ya kammala ramukonsa kafin yayi sittu shawwal. Saboda cikar bayanin da hadisin yazo dashi cewa "WANDA YA AZUMCI RAMADHAN, SANNAN YABI BAYANSA DA KWANA SHIDA DAGA SHAWWAL.......... ".
Saboda cikar fa'idah ne Malamai suka ce anfi son mutum ya kammala ramukonsa tukun... Amma idan mutum yana da ramukon masu yawa akansa, kuma gashi ba ya son falalar sittu shawwal ta wuceshi, to zai iya azumtar sittu shawwal din sannan daga baya ya rama abinda ake binsa.
WALLAHU A'ALAM.