Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria yayi alkawarin cewa, gwamnatinsa zata yi iya kokarinta da yarda Allah na kwato yan matan.
Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria yayi alkawarin cewa gwamnatinsa zata yi iya kokarinta na sake kwato yan matan Chibok daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram
Shugaban yayi wannan alkawari ne a yayinda aka ciki kimamin kwanaki 502 tun lokaci yan kungiyar Boko Haram suka sace yan matan daga makarantar su a garin Chibok jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria.
Gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ne ya wakilci shugaba Buhari a fadar gwamnatin jihar Borno a lokacinda ya gaiyace iyayen yan matan domin gabatar da sakon.
Shugaba Buhari ya baiwa iyayen hakuri. Wasu daga cikin iyayen yan mata sun baiyana ji dadin jin wannan sako kuma suka baiyana fatar Allah yasa ba irin alkawuran da aka yi musu a baya bane. Alkawuran da ba'a cika ba.
Kimamin kwanaki dari biyar da biyu, ke nan tun lokacinda yan Boko Haram suka sace yan matan daga makarantarsu a garin Chibok, jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria