Mutane 20 ne guguwar ta kashe yayin da gidaje da gadoji da hanyoyin mota da dama sun lalace. Wasu jama'ar dubu 150 suka rasa wutar lantarki a Jamhuriyar Dominika.
Mahaukaciyar guguwa hade da ruwan sama da iska mai karfin gaske wadda ta ratsa kasar Haiti ta kashe mutane 20 a tsibirin Dominika yayin da wasu da dama aka rasa inda suke ,Roosevelt Skerrit wanda shi ne firaministan kasar, ya ce ''Ina cikin damuwa da bacin rai sossai a wannan jawabi da nake yi zuwa gareku a sakamakon wannan bala'i da ya fada wa kasarmu,dole sai mun nuna dangana da kuma yin juriya.''
Ruwa kamar da bakin kwarya da aka rika shekawa ya haddasa ambaliya tare da zubar laka wacce ta bizne wasu mutanen da ransu. A halin da ake ciki hukumomi sun takaita zirga-zirgar jama'a kana, sannan kuma an rufe makarantu tare da haramtawa jiragen ruwan motsawa daga bakin teku.
Title :
Guguwa ta yi kisa a Dominika
Description : Mutane 20 ne guguwar ta kashe yayin da gidaje da gadoji da hanyoyin mota da dama sun lalace. Wasu jama'ar dubu 150 suka rasa wutar lanta...
Rating :
5