Guguwar mai suna Typhon ta ratsa kasar ta Taiwan a wannan assabar inda ta kashe mutane hudu tare da haddasa katsewar wutar lantarki a gidaje sama da dubu dari bakwai.
A Taiwan wata mahaukacciyar guguwar mai suna Typhon da ta ratsa kasar a wannan assabar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da katse wayoyin wutar lantarki da kuma jefa gidaje sama da dubu dari bakwai a cikin duhu. Mahaukacciyar guguwar ta Typhon wacce ke gudun kilomita 200 a cikin aa daya ta zo ne tare da rakkiyar ruwan sama mai karfin gaske da aka kiyasta ya kai mita guda a mizanin ma'auna ruwan sama.
A Taipeh babban birnin kasar mahaukacciyar guguwar ta tone karafinan gine-gine da manyan itatuwa, wanda ya sanya hukumomin birnin daukar matakin dakatar da sufurin motocin safa-safa na bus dama na jiragen kasa. A na sa ran dai guguwar za ta susuce tare ma da ficewa daga kasar nan zuwa tsakiyar yini,kuma za ta isa a wasu Jihohin kasar China inda tuni hukumomin kasar suka kwashe mutane sama da dubu 160 daga yankunan da ake sa ran guguwar za ta bi.
Title :
Guguwa ta kashe mutane a Taiwan
Description : Guguwar mai suna Typhon ta ratsa kasar ta Taiwan a wannan assabar inda ta kashe mutane hudu tare da haddasa katsewar wutar lantarki a gidaje...
Rating :
5