Assalamu alaikum 'Yan uwa.
Akwai wata MUMMUNAR BARNA TA FASIKANCI wacce ta bullo kwanan nan cikin al'ummah.
Zaka ga samari da 'yanmata (Musamman wadanda aka sa ranar aurensu) suna zuwa suna daukar wasu munanan HOTUNA MARASA KYAN GANI.
Ko kaga sun rungumi juna, ko kaga Saurayin ya dora fuskarsa akan Qirjin budurwar, ko kaga budurwar ta zauna akan cinyar saurayin, ko kuma ka ganta ta dora tafin hannayenta akan kafadar Saurayin ko Kan Qirjinsa.
Wannan ba Qaramar Fitsara da Fasikanci bane, Kuma WALLAHI BIL-LAHIL AZEEM Duk ma'auratan da suka aikata irin wannan kafin aurensu, to SUN ZUBAR DA ALBARKAR AURENSU. Kuma sunci amanar Allah da Manzonsa, sun wulakantar da tarbiyyar addininmu na Islama.
Haramtaccen Jima'i ba shine kadai ZINA ba. kallon da ya sa'ba ma shari'a ma ZINA ne. Ta'ba jikin juna kafin aure ma ZINA ne. Yin kalamai na BATSA ko zantukan motsa sha'awa shima ZINA ne.
Duk Ma'auratan da suka aikata 'daya daga cikin wadannan, to tabbas SUN ZUBAR DA ALBARKAR ZURIYAR DA ZASU HAIFA.
Nagartar iyaye da kuma albarkarsu tana shafar duk irin zuriyar da zasu haifa. Hakanan lalacewar iyaye da kuma fasikancinsu yakan shafi irin zuriyar da zasu haifa.
Kunyi zina kafin aurenku, kuma yanzu kuna tsammanin zaku haifi Hamshakan Malamai da Mahaddatan Alqur'ani?
Yayi fasikanci dake tun kina gidanku, ya riga ya sanki 'ya mace tyn kafin aure, kuma kina zaton zai rike ki da mutunci bisa amana, bayan ya riga yaci amanar Allah da Manzonsa?? Ta ki amanar ne ba zai ci ba??
Duk abinda kuka shuka shi zaku girba.. komai kankantarsa komai girmansa.