Alokacin da Manzon Allah (saww) ya tafi yakin Tabuka, da dare yayi, Sahabbai duk sunyi barci.
Abdullahi bn Mas'ud (ra) yace: "Na tashi zuwa wajen Shimfidar Manzon Allah (saww) na duba ban ganshi ba, da na dora hannuna akan wajen kwanciyarsa sai naji sanyi (alamar da taje nuna cewa ya dade da tashi kenan).
Na tafi wajen Shimfidar Sayyiduna Abubakar, shima ban sameshi akan shimfidarsa ba.. Sai na wuce zuwa kan shimfidar Umar bn Khattab shima ban ganshi akan shimfidarsa ba.
Chan sai na hango wani haske daga Qarshen Sansanin nan, daga gefen Askarawan. Don haka na tafi wajen hasken don in dubo.
Da naje sai naga an tona Qabari, kuma Manzon Allah (saww) ya shiga cikin Qabarin. Kuma ga wata gawa nan akwance agefe an nadeta da likkafani.
Sayyiduna Abubakar da Umar suna gefen Qabarin sai Manzon Allah (saww) yace musu "KU MIKO MIN SAHIBIN NAN NAKU".
Yayin da suka mikoshi sai Manzon Allah (saww) ya saukar dashi acikin Qabarinsa. Sannan sai idanuwansa suna zub da hawaye.
Ya juya wajen Alkibla, ya cira hannayensa masu albarka yana addu'a yana cewa:
"YA UBANGIJI, NI NA WUNI INA YARDA DASHI. KAIMA KA YARDA DASHI. YA UBANGIJI, NA WUNI INA YARDA DASHI, KAIMA KA YARDA DASHI. YA UBANGIJI NA WUNI INA YARDA DASHI, JAIMA KA YARDA DASHI.".
Sai na tambayesu Shun wanene wannan da ya rasu?".
Sai aka ce min "Dan uwanka ne mai suna ABDULLAHI DHUL BIJADAINI".
Wallahi sai naji ina ma nine wannan!!!