Everton ta amince da mai tsaron bayanta John Stone ya bar ta, bayan da Chelsea ta nace sai ta sayi dan wasan.
Chelsea ta fara taya Stone kan kudi £20m da kuma £26m sannan ta kara tayi na uku kan kudi da ya kai £30m.
Everton ta ci gaba da nanata cewar ba za ta sayar da dan kwallon ba a bana, kuma kungiyar ta ki cewa komai kan bukatar da Chelsea ta gabatar mata.
Stone ya koma Everton ne daga Barnsley a watan Fabrairun 2013 kan kudi £3m.
Title :
Everton ta amince Stone ya bar kungiyar
Description : Everton ta amince da mai tsaron bayanta John Stone ya bar ta, bayan da Chelsea ta nace sai ta sayi dan wasan. Chelsea ta fara taya Stone ka...
Rating :
5