Enyimba ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 24 da suka buga a Aba ranar Laraba.
Enyimba ta ci kwallon ne daga bugun fenariti a minti na 28 da fara tamaula, kuma Ifeanyi George ne ya zura kwallon a raga.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga Wikki Tourist ta zura kwallaye 2-0 a ragar Abia Warriors, yayin da El-Kanemi Warriors da Warri Wolves suka tashi wasa babu ci.
Heartland kuwa doke Kwara United ta yi da ci daya mai ban haushi, itama Dolphins 1-0 ta samu nasara a kan Sunshine Stars, kuma fafatawa tsakanin FC Taraba da Bayelsa United suka tashi kowa yana nema.
Za a karasa sauran wasannin makwo na 24 ranar Alhamis tsakanin Sharks da Lobi Stars da kuma karawa tsakanin Ifenyiubah da Akwa United.
Giwa FC za ta karbi bakuncin Enugu Rangers a Jos, sai kuma Nasarawa United da za ta ziyarci Shooting Stars.
Ga sakamakon wasan makwo na 24 da aka buga:
El-Kanemi 0-0 Warri Wolves
FC Taraba 0-0 Bayelsa United
Dolphins 1-0 Sunshine Stars
Wikki Tourists 2-0 Abia Warriors
Heartland 1-0 Kwara United
Title :
Enyimba ta samu nasara kan Kano Pillars
Description : Enyimba ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 24 da suka buga a Aba ranar Laraba. Enyimba ta ci kwal...
Rating :
5