A Nigeria, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kai karar tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan tsaron Kanar Sambo Dasuki mai ritaya a gaban kotu bisa zargin sa da mallakar bindigogi ba bisa ka'ida ba.
A watan Yuli ne hukumar DSS ta kai samame a lokaci guda, a gidaje uku na Sambo Dasukin a Abuja da kuma Sakkwato, inda daga bisa hukumar ta ba da sanarwar cewa ta gano wasu manyan makamai da motocin sulke da ka iya yin barazana ga tsaron kasa.
Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ya rasa mukaminsa ne bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar da ya gada daga gwamnatin shugaba Jonathan.
Daga bisani an maye gurbin su da wasu a kokarin da shugaban kasar ya ce yana yi na magance hare haren ta'addanci daga kungiyar Boko Haram.