Wani mahaifi a kasar Ghana ya bukaci dansa ya dawo gida, bayan da ake tunanin cewar ya fice daga kasar domin shiga kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci.
Alhaji Abdul Latif Alema ya ce, dansa mai shekaru 25 da haihuwa, mai suna Muhammed Naziru Nortei Alema ya aiko masa da sako a WhatsApp kwanaki tara da suka wuce a kan cewar, ya hade da kungiyar IS kuma tun daga lokacin ba a sake ganinsa ba.
A cikin sakon ya ce: "Zuwa ga mahaifina da mahaifiyata, ka da ku damu a kan danku, saboda ban yi laifi ba, ina neman gafara daga Allah ne."
Shekaru biyu da suka wuce ne, Mohammed Naziru ya kammala jami'ar kimiyya da fasaha watau Kwame Nkrumah University of Science and Technology da ke birnin Kumashi.
Mahaifinsa, Alhaji Abdul Latif Alema ya shaida wa wakilinmu Iddi Ali cewa ranar biyu ga wannan watan na Agusta ita ce ranar karshe da ya yi ido-biyu da dan nasa.
"Kamar an yi mutuwa a gidana. Babu wanda ke cikin farin ciki. Kuma mahaifiyarsa ta na ta kuka, da yin azumi domin ya dawo," in ji Alhaji Alema.
Hukumomin tsaron Ghana dai sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin tare da wasu kuma da suka samu labarin cewa suma sun fita daga kasar domin shiga kungiyar ta IS.
Title :
Dan Ghana ya hade da kungiyar IS
Description : Wani mahaifi a kasar Ghana ya bukaci dansa ya dawo gida, bayan da ake tunanin cewar ya fice daga kasar domin shiga kungiyar IS mai da'aw...
Rating :
5