Musulmi sun fi riko da koyarwar
Al-Masihu fiye da Kiristoci ...
Shahararren dan wasan tamaula
(kwallon kafa) dan kasar Togo,
Emmanuel Adebayor, ya watsar da
addinin Kiristanci ya rungumi
addinin Musulunci. A cewarsa ya
lura cewa Musulmi ne suka fi koyi
da kuma aiki da koyarwar Al-
Masihu (Annabi Isah - A.S.) fiye
da Kiristocin da ke bugun gaba da
cewa Al-Masihun nasu ne.
A wani faifan bidiyo da ya fitar a
shafin YouTube, Adebayor ya
rattabo dalilai 13 da suka sanya
shi rungumar addinin Musulunci.
Dalilan su ne:
1.
Al-Masihu ya koyar da cewa Allah
daya ne, kuma shi kadai ne abin
bauta, kamar yadda ya zo a cikin
Deut 6:4 da Mark 12:29. Haka ma
Musulunci ya koyar, kamar yadda
ya zo a cikin Qur'an 4:171.
2.
Al-Masihu ba ya cin naman alade,
kamar yadda ya zo a cikin
Leviticus 11:7. Musulmi ma ba su
cin naman alade kamar yadda ya
zo a cikin Qur'an 6:145.
3.
Al-Masihu yakan gayar da mutane
da sallama, 'Assalamu alaikum,'
kamar yadda ya zo a cikin John
20:21. Wannan ya yi daidai da
dabi'un Musulmi.
4.
Al-Masihu yakan yawaita fadar, 'In
Allah ya yarda - In Sha Allah.'
Kamar yadda koyarwar Musulunci
take a cikin Qur'an 18:23-24.
5.
Al-Masihu yakan wanke hannuwa
da fuska da kafafunsa kafin yin
duk wata ibada. Haka Musulmi ke
yi kafin su yi sallah.
6.
Al-Masihu da duk wasu Annabawa
da aka ambata a cikin Bayibul
(Bible) sukan yi sujuda ga
Ubangiji, goshinsu a kasa (duba
Mathew 26:39). Musulmi ma na
sujuda ga Ubangiji kamar yadda
ya zo a Qur'an 3:43.
7.
Al-Masihu ya tsayar da gemu
kuma yana yafa mayafi bisa
kansa. Haka koyarwar Musulunci
take, maza su tsayar da gemu, su
rika yin rawani.
8.
Al-Masihu yana matukar kiyaye
dokokin Allah, ya kuma yadda da
dukkan Annabawan da suka zo
kafin shi (duba Mathew 5:17).
Musulmi ma sun yadda da dukkan
Annabawa (duba Qur'an 3:84 da
2:285).
9.
Maryama, mahaifiyar Al-Masihu,
tana sanya tufafin da ke rufe
ilahirin jikinta, kuma ta rufe kanta
da mayafi, kamar yadda ya zo a
Timothy 2:9, Genesis 24:64-65 da
Corinthians 11:6. Haka matan
Musulmi kan yi irin wannan shigar
kamar yadda ya zo a Qur'an
33:59.
10.
Al-Masihu da wasu Annabawa da
aka ambata a Bayibul, sukan yi
azumi na kwanaki 40 (duba
Exodus 34:28, Daniel 10:2-6 da
Mathew 4:1). Haka Musulmi kan yi
azumin kwanaki 30 a watan
Ramadan (duba Qur'an 2:183),
wasu ma har sukan kara da azumi
6 bayan watan Ramadan domin
neman karin lada.
Title :
DALILAI 10 DA SUKA SA NA MUSULUNTA - Emmanuel Adebayor
Description : Musulmi sun fi riko da koyarwar Al-Masihu fiye da Kiristoci ... Shahararren dan wasan tamaula (kwallon kafa) dan kasar Togo, Emmanuel Ade...
Rating :
5