Masu aikin ceto a tekun Baharrum sun ce sun fitar da rai daga samun wani da rai a cikin mutanen da wani jirgin ruwa ya nutse da su a kusa da kasar Libya.
Jirgin da ya nutse ya na dauke da 'yanci rani 600 ne a cikin sa.
Masu tsaron tekun Italiya da kuma hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta majalisar dinkin duniya sun ce ya zuwa yanzu an ceto mutane 400 yayinda aka gano gawawwaki 25.
Jiragen ruwa 7 da kuma jirage masu saukar ungulu ne suka isa wurin domin aikin ceton.
Jami'ar yada labaran hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta majalisar dinkin duniya Melissa Fleming ta ce mutane ne suka yi yawa a jirgin da ya nutse.
'Yan ci-rani sama da 2,000 ake zaton sun nutse a wannan shekarar, a yunkurin tsallaka tekun zuwa Turai.