Dan kwallon Chelsea, Juan Cuadrado ya sanya hannu a yarjejeniyar komawa taka leda aro a Juventus bayan kusan watanni takwas da ya yi a Stamford Bridge.
Dan kwallon Colombia din ya koma Chelsea daga Fiorentina a watan Fabarairu a kan kudi sama da fan miliyan 23, zai yi wa Juventus wasanni aro zuwa karshen kakar bana.
Wasanni 15 kawai Cuadrado ya buga a Stamford Bridge kuma tun da Pedro ya zo daga Bercelona aka soma tunanin dan Colombia din zai bar Chelsea.
Daruruwan magoya bayan Juventus ne suka tarbi Cuadrado a Italiya domin soma taka leda a gasar Serie A.
Title :
Cuadrado ya koma Juventus da taka leda
Description : Dan kwallon Chelsea, Juan Cuadrado ya sanya hannu a yarjejeniyar komawa taka leda aro a Juventus bayan kusan watanni takwas da ya yi a Stamf...
Rating :
5