China ta sake rage darajar kudinta, watau Yuan, lamarin da ya kara kawo tangal-tangal a kasuwar hada-hadar kudade ta duniya.
Babban bankin kasar, ya ba da izini ga masu hada-hadar kudin kasar da su rage farashin da suke sayar da shi, da kashi daya da digo shida.
Faduwar kudin na Yuan zai zamewa sauran kasashen nahiyar Asia ala-kakai, domin kuwa hakan na nufin kayan da kasar ke samarwa za su fi na sauran kasashen yankin araha.
Rage farashin kudin ya sa kasuwannin kudi na Turai da Asia sun rude.
Matakin ya janyo sabuwar tankiya tsakanin China da Amurka, wacce ta dade tana cewa rage darajar kudin China, yana bai wa 'yan kasuwar da ke fitar da kayayyaki daga kasar a kan takwarorinsu na kasashen duniya
Title :
China ta rage darajar kudinta 'Yuan'
Description : China ta sake rage darajar kudinta, watau Yuan, lamarin da ya kara kawo tangal-tangal a kasuwar hada-hadar kudade ta duniya. Babban bankin...
Rating :
5