A ranar Lahadi 23 ga watan Agusta, Sanata shehu Sani ya bayyana cewa Majalisar Dattawa a shirye take data goyi bayan shugaba Buhari akan yakar rashawa da cin hanci.
A cewar jaridar Premium Times, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Shehu sani yace: “An dade ana yi ma Yan Najeriya mulkin kama karya. Amma shugaba Buhari ya nuna dagewar shi wajen yakar rashawa. Majalisar Dattawa zata taimaka mashi kwarai.
“Buhari kuma ya nuna dagewar shi wajen ganin ya kawo karshen Yan Boko Haram. Majalisar Dattawa zata taimaka mashi domin ganin cewa an kawo karshen Boko Haram, sannan kuma Yan gudun hijira su koma gidajen su.
Title :
Buhari Ya Nuna Dagewa - Shehu Sani
Description : A ranar Lahadi 23 ga watan Agusta, Sanata shehu Sani ya bayyana cewa Majalisar Dattawa a shirye take data goyi bayan shugaba Buhari akan yak...
Rating :
5