Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa kan rikicin mulkin da ake fuskanta a kasar Guinea Bissau inda ya bukaci al’ummar kasar su mutunta kundin tsarin mulki.
Mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina yace shugaba Buhari ya tura tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zuwa kasar dan sasanta shugaba Jose Mario Vaz da Firaminsita Domingos Pereira.
Akan hanyar sa ta zuwa kasar, Obasanjo ya gana da shugaban kasar Senegal Macky Sall dake shugabancin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, dan yi masa bayani.
Title :
Buhari Ya Damu Kan Rikicin Mulkin Kasar Guinea Bissau
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa kan rikicin mulkin da ake fuskanta a kasar Guinea Bissau inda ya bukaci al’ummar ka...
Rating :
5