Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da karin jiragen yaki zuwa arewa maso gabashin kasar.
Wannan dai na zuwa ne bayan umarnin da shugaban na Najeriyar, Muhammadu Buhari ya ba wa sabbin hafsoshin tsaron kasar da su kawo karshen Boko Haram cikin watanni uku.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore, Dele Alonge ya fitar, ta ce an tura jiragen yakin ne zuwa yankin na arewa maso gabashin kasar a lokacin da babban hafsan sojin saman kasar, Air Marshal Sadiq Abubakar ya kai ziyarar gani da ido a yankin.
Sanarwar ta ce jiragen sun hada da mai saukar ungulu samfirin Mi-24 da Agusta 109 LUH da Supa Puma da kuma wani jirgin mai saukar ungulu na sintiri kirar ATR-42 wanda aka kai shi gyara a baya.
A ranar Alhamis ne dai shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa sabbin hafsoshin tsaro kasar da ya rantsar a ranar umarnin da su tabbatar sun murkushe kungiyar Boko Haram cikin watanni uku.
Title :
Boko Haram: An aika jiragen yaki arewa maso gabas
Description : Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da karin jiragen yaki zuwa arewa maso gabashin kasar. Wannan dai na zuwa ne bayan umarnin da shugaba...
Rating :
5