Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan batutuwa da dama da suka shafi tattalin arziki da yaki da ta’addanci da wanzar da zaman lafiya a kasashen Afrika.
Ban ya kawo ziyara ne a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya a karshen mako domin tunawa da mutanen da aka kashe a harin da Mayakan Boko Haram suka kai ofishin Majalisar Dinkin Duniya a 2011.
A cikin jawabinsa, Ban Ki-moon ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta taimakawa Najeriya kan yunkurin gwamnatin Muhammadu Buhari na kakkabe ayyukan Boko Haram.
Ban ya kuma bukaci shugaba Buhari ya magance matsalolin da suka haifar da rikicin Boko Haram da suka hada da magance rashin ayyukan yi tsakanin matasa.
A nasa bangaren, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da ziyarar Ban Ki-moon wanda ya danganta a matsayin mataki na samun taimakon kasashen duniya kan yaki da Mayakan Boko Haram.
Buhari kuma ya gode wa Ban Ki-moon da gayyatarsa da ya yi zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a ranar 27 ga watan Satumba.
Title :
Ban Ki-moon ya yi alkawalin taimakawa Najeriya
Description : Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan batutuwa da dama da suka shafi tatta...
Rating :
5