A yau Lahadi ne sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, zai kawo ziyara a Najeriya, Ziyarar dake zuwa shekaru uku da kai wani hari bam a Ofishin majalisar ta Dinikin Duniya dake Abuja.
A wannan ziyara Ban Ki Moon, zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, daya karbi madafun ikon kasar a ranar 29 ga watan Mayu shekarar 2015, zai kuma ganawa ta musaman da wasu Gwamnoni dama yan kasuwa.
Yayi ziyarar, Ban zai aza fure, don yi tuni dama cika shekaru 4 da harin da aka yi amfani da wata motar zuwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja.
Tuni kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin harin, da ya hallaka mutane 21 a wancan lokacin.
Tun bayan da shugaba Buhari ya karbi madafun ikon kasar, ake ci gaba da yakar mayakan na Boko Haram, da zuwa yanzu suka hallaka dubun dubatar mutane a kasashen yammacin Afrika da suka hada da Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Chadi.