Wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a kusa da kasuwar Sabon Gari wadda ke yankin Damboa zuwa Biu a jihar Borno inda mutane 28 suka rasu.
Jami'in hukumar ba da agajin gaggawa watau NEMA, Mohammad Kanar ya shaidawa manema labarai cewar baya ga mutane 28 da suka rasu wasu kuma 79 sun samu raunuka.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a bangaren wurin sayar da kayayyakin wayar salula na kasuwar.
Jami'an tsaro a yankin suma sun tabbatar da afkuwar lamarin amma sun ce basu da adadin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Lamarin ya auku ne da rana a lokacin da mutane ke tsakiyar hada-hada.
Tun a watan Mayu da shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, mutane kusan 800 sun rasu sakamakon hare-haren da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai.
Jihar Borno ta kasance cibiyar 'yan Boko Haram wadanda suka hallaka dubban mutane tare da raba mutane fiye da miliyan daga muhallansu.
Title :
Bam ya hallaka mutane 28 a kusa da Damboa
Description : Wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a kusa da kasuwar Sabon Gari wadda ke yankin Damboa zuwa Biu a jihar Borno inda mutane 28 suka rasu...
Rating :
5