Sarautar Uban dawaki babbar sarauta ce a
garin fandagori can cikin jihar naija. Babban gari
ne wanda al'ummar cikinsa suka bunkasa wajen
noma da kiwo. Gidan uban dwk Alh Awaisu
Malami katafaren gida ne cike da zuri'a masu
yawa na kannensa guda 2 kuma shine babbansu
kat!
Sassan sa yafi na kowa girma da tsari ginin
zamani. Matarsa daya Haj Halima da yaya maza
uku a jere. Abdulkadeer, Abdulkareem da
Abdulrahman sai kandensu "ya mace tilo a
cikinsu Sakina, sunan mahaifiyar uban dwk
gareta shiyasa suke kiranta "Mama".
Santaleliyar yarinya wacce Allah yayiwa sura
tamkar ita tayi kanta kusan zuri'ar gidan haka
suke da kyau na fulani. Amma ita mama ta fita
daban wajen cikar sura daka gganta dole
gabanka ya fadi sbd tsabar kyau.
Shiyasa tun shekarunta basu kai ko'ina ba samari
suka yanyameta kowa na so, musamman cikin
gidansu watau yan'uwanta abin har yana so ya
zama rigima a tsakaninsu.
Saida Uban dwk da kansa ya tara su ya soke
maganr soyayya da Mama ya kuma kar wanda ya
kara kiranta da sunan tadi. Yayi haka ne don a
sami masalaha da zaman lfy. Allah kuwa ya
taimaka kowa ya gama bacin ransa ya hakura.
Baya ga haka yana ganin Sakeena bata kai
shekarun da zata tsoma kanta kogin soyayya ba
alhali tana tsaka da karatunta mafarin kenan da
zata tafi babbar sakandire yayi kokari ya samar
mata makarantar kwana ta yanmata dake bakori
(FGGC Bakori) Sannan hankalinsa ya kwanta
amma wann hukunci nasa yayiwa wasu daga
cikin iyaye mata ciwo har suna ganin sbd kyaun
da Mama take dashi ne yasa ake wulakanta
yayansu suka rinka ganin kamar suna sn su dauki
dogon buri ne su dora mata.
Tabbas uban dwk nada buri akan yarsa tilo mace
saidai yasha bamban da irin burin da matan
gidan ke nufin ciki zukatansu wanda bazai wuce
ya aurar da ita ga hamshakin me kudi ba ko
basarake. Shi burinsa yarsa tayi zurfin karatu
kamar sauran yayyinta maza wadanda a halin
yanzu Abdulkadeer major nr na soja,
Abdulkareem accountant ne a CBN, sai
Abdulrahman dake NYSC a Jalingo. Ya kuwa
lashi takobin ko bashi da rai yan'uwanta su cika
masa wann buri nasa.
Kwanci tashi Mama ta shiga SS2 kuma yau
sukayi hutun 2nd term tun safe Uban dwk ya tura
drivernsa ya daukota, basu iso fandagori ba sai
bayan la'sar kowa na ta murna musamman yara
da suka yanyameta suka kwashe mata kaya
zuwa sassansu. Ta shigo da sallama Ummanta ta
tarbeta ta rungumeta, ta shiga sauran sassan ta
gaishesu, Salisu da Danlami kadai ta samu acikin
samarin sassan.
Ta zauna suka taba yar hirar skul sannn ta tashi
koma sassansu tana shiga ummanta tace
Abbanki na nan ya dawo ta wuce da sauri ta
sameshi a falonsa, bakinta har kunne ta dan
rankwafa tace Allah ya taimaki mai martaba!
Fara'arsa ta karu: Allah yabar min Mamana na
shigo akace kin shiga sassa. Ta zube gabansa
tace eh naje gaishesu ne, ina yini Abba? Lfy lau
ya karatu? To mungode Allah, yace ina report
sheet a kawo na gani. Ta mike taje ta kwaso duk
takardun yayi ta dubawa yana fadin da kyau!
Bayan ta kammala ya dubeta kinyi kokari sosai
Mamana na baya miki amma har yanzu kina da
yar matsala a biology sai kin kara bada himma
kinsan dalili? Ta kada kai yace kara matsowa kiji
ta matso kusa dashi sosai kafin yace: buri na ki
zama likita Mamana, sbd a rayuwa ta ina
sha'awar in ga ya mace likita, abin yana burgeni
kwarai, shiyasa tun ranar da Allah ya bani ke
nake ta addu'ar Allah ya raya minke in samu in
cika burina, ko kuwa ke bakya sha'awa? Tace
sosai ma nakeson zama likita Abbana. Kuma
I.S.A zan kara himma don ganin na gama da
biology. Ya dafa kanta cike da farin ciki yace
yauwa Mamana, Allah yai miki albarka tace
ameen Abbana. Daga nan suka ci gaba da
hirarsu saida akayi sallama dashi ya tashi ya
shiga babban zaure inda Majalisarsa ke taruwa.
Mamana ta koma gurin Ummanta a kicin suna
aikin abinci tana bata labarin abnd Abbanta yace,
Umma tace yallabai kenan Allah dai ya cika
masa wann buri nasa tace I.S.A Umma saina
zama likita. Tace Allah ya yarda wai waya gane
min Mama da farafen kayan nan? Mama tana
dariya tace na dan ratayo wann abun da suke
sawa a kunne ina takawa ana ga Dr Sakeena nan
zuwa. Suka fashe da dariya. Washegari misalin
10:am Mama ta fesa ado da koriyar atamfa
sannn ta dora after dress ta yafa mayafinta ta
sami Umma a daki, sai ina? Zani gaida Inna
saude ne. A'a kice dai zaki gun Baraka.
Tayi dan murmushi Umma ai duk dayane Idan na
gaida Inna ta sai muyi hira da Baraka kawata...
Uhummmn... To kodai lauya zaki zama a fasa
likitan nan? Tayi dariya wai kinaso ki hada ni da
Abba kenan.. Lallai kam to kice ina gaida Sauden
idan ta gama dinkunan ta baki kizo min dasu,
shikenan amma ina fata akwai nawa aciki.
Umma tace babu naki aciki duk nawa ne,
Mama ta dan kirne fuska kai umma ai kuwa zan
zabi daya aciki, tace duk zannuwa ne ciki da
alakum rigunan kuma masu hannu ne, zan canja
style ni inaso a haka, to ban yarda ba ki anso min
kayana kawai idan ta gama. Ta jinjina kai
shikenan umma nina tafi, adawo lfy karki dade...
Ta saba jakarta tana fadin to Umma..
Salis ne zaune a kofar gida tana fitowa ya kare
mata kallo sama da kasa kafin yace sai ina
kuma? "Gidan Inna Saude zanje" 'Okay na kuwa
ga Baraka jiya itama ta dawo". Ya mike muje in
rakaki ko bakiso? "Muje mana ta wuce ya biyota
suka jera. Wai Mama meyasa Abba yake takuraki
dayawa? "Kamar yaya?" Baya son kina kula
samari kin kuwa san har yanzu yaya Ali yana
sonki? Ta dube shi farin sani kuwa tunda yana
gaya min a sace amma fitinar duk waya fara
daukota?
Yace a'a ba don muna uwa daya uba daya dashi
ba, abnd yaya Sa'ed yayi bai kyauta ba, tunda
yasan shi yana sonki menene na shi na shigo
nemanki? Ya fa san halin Yaya Ali ba hakuri ne
dashi ba yanzun nan sai ya nuna maka hauka. Ta
dan tabe baki tace hmmmnn... Kai nifa karatu
ma zanyi dama sun sa ransu a inuwa, babu
wanda zan aura acikinsu koda Abba bai dakatar
dasu ba.. Ya zura mata ido kina wulakanci Mama
kice dama kema ba sonsu kike ba? Baka gane
ba.. Me kikeso ki fada? Karatu zai hanaki aure
ne? Ta kada kai nutsuwa nafi bukata sbd
karatuna mai son nutsuwa ne.. Me zaki karanta?
"Akikin likita" ya ware ido Uhmmnn.. Dokta
Sakeena kenan!
Tayi murmushi har kasa naji gingiringin! Yayi
dariya daidai lokacin da suke tsayawa gefen
babban titi.. To Dr Sakeena ni anan zan juya..
"Ngd ai kaga har nayi sauri da yake ana hira"
yace dadin abokin rayuwa kenan, don ma ba Ya
Ali bane tayi dan tsaki get lost donAllah ka
rabani da wann zancen, yana dariya ta tsallaka
titi ta barshi hanya shi kuma ya juya ya koma
gida.
Mota yake kakkabewa ya cire shimfidar foot mat
lokacin da Mama tazo wucewa, yayi tsaye yana
kallon wata surar da bai taba gamo da irin ta ba..
Kai ya kasa daurewa saida yayi mata sallama..
Ta dago ido ta dube shi tare da amsawa, sautin
muryarta ya kara rikita shi ya bita da sauri
donAllah ko zaki 5mins kadai in tambayeki? Ta
tsaya caka tana dubansa, dogo ne sosai "Allah
yasa na sani" yace donAllah anan garin kike?
Tambayar tasata a mamaki tace eh mana, amma
ban taba ganinki ba sai yau. Tace kasan daurowa
take , gsky ne, ah suna nan Al-Ameen ina minna
amma nan gidan kaka ta ne, na kawo Mamana
ne ma yanzu sau dayawa ina zuwa nan shiyasa
kikaji na tambayeki.
Haka ne yau ne Allah ya nufa zamu hadu. Ya
sauke numfashi gsky ne, allah ya hadamu kuma
take nan kin kwanta min a rai ko zan san
sunanki? Ta dan kauda kai yanayin mata saida
gabansa ya fadi tsoro ya kamashi kada ya sha
kayi. Ya marairaice dan daure ki gaya min ba don
hali na ba, hali? Nasan halinka ne? Yace na mita
da bakin naci! Tayi dan murmushi Sunana
Sakeena' kai! Sunan nan ya dace da kykkyawar
fuskar nan! Anan unguwar kike? Ta dan kada kai
can gidan zani wajen kanwar Ummana, ok to
gidanku fa?
Ta yatsuna fuska alamun ta kosa ta wuce, harta
fara takawa ya biyota na dameki ko? Yi hakuri so
ne ya kamani ki taimake ni, ta tsaya ta dube shi
da idanuwanta farare kal dasu tace kasan Uban
dawaki? Can tsallaken titi kenan? Ni yarsa ce
idan kasan gidan, nan ne gidan mu saidai akwai
matsala. Ya hadiye murmushin sa Matsala? Na
shiga uku a ina matsalar take? Tace Abbana
baya bari azo zance wajena yace sai na gama
karatu hasali ma bording skul nakeyi daga hutu
sai hutu ake ganina, ya danyi shiru jim kafin yace
to ya za'ayi yanzu Sakeena?
Gsky ba da wasa nakeyi ba ya kike ganin za'ayi?
Tace ban sani ba amma ina ganin hakuri zai fi
kyau, mu saurari lokacin kammala karatun, ba kai
kadai bane akwai wasu wadanda suka rigaka
magana kuma sun hakura. Yace su zasu iya ne
nikam bazan iya ba Sakeena! Ina sonki sosai
babu abnd nake rayawa a cikin rain aface na
aureki. Ta dan kara dubansa sai taji ya fara
zama cikin ranta. Matsalar kawai batasan yanda
zatayi dashi ba har tace yaje gidansu.
Don haka tace kayi hakuri Al-Ameen.. Ta wuce
da sauri ta barshi yana kira Sakeena! DonAllah
tsaya mana kiji.. Gidaje biyu ta wuce na ukun
shien nasu Inna Saude. Ta sa kai ciki tare da
sallama baraka dake tsaye tsakar gida tana gyara
zaman mayafinta ta juya da sauri baki sake suka
rungume juna.. Gidanku zan tafi yanzu a haba?
Wllh yanzun nan kewa Inna sallama har ta bani
dinkunan Umma tace dama nima ta aikoni
akansu, ina Innar? Tana ciki suka shige tare Inna
tace au Mama ce? Har kin rigata kenan tana
dariya ta zauna sannu Inna ina kwana? Ta amsa
lfy lau an dawo lfy? Tace wllh lfy lau inna, kinga
dinkinta dama za'aje kai mata Mama ta fiddo su a leda ta daddaga kai amma atamfofin masu kyau. Suka dan taba hira suka wuce dakin
Baraka kowacce ta cire after dress.
Mama ta fada katifa tace tun dazu ya kamata in
shigo gidan nan bakon unguwarku ya tare ni.
Bako? A ina?tace oho! Wai nan gidan Alh lado
suke cewa ko? Eh nan ne gidan kakarsa Al-
Ameen yace min sunansa, bakinta har kunne ta
jawo hannunta suka tafa ban mu kashe yar'uwa
bakar fata kice kinyi gamao da katar. Likita
bokan turai yau shiya kawo Maman tasa kenan.
Ta ware ido kina nufin Dr ne? Kwarai kuwa ko
bai kammala ba kiris ya rage, don tuntuni naji
ana fadin sabis yake, ta kama baki har kin kara
min son shi ina ma ace wann abu ya tabbata
kusa bikin likitoci, au kema likitance?
Tace zauna nan in gaya miki jiy-jiya Abba ya
gaya mina bnd zan karanta kenan, kuma gsky Al-
ameen yayi min matsalar kawai Abba. A'a ina
cewa ya soke maganar su Ya Ali? Eh mana to ai
baki sani ba soke maganar ita ta janyo min
tsiyar. Kina zaton su kawu baza suji haushi ba?
Ance karatu zanyi kuma wani yazo an bashi? Ai
sai Umma tayi bakin jini acikin gidan. Bansan
yanda zanyi ba shi kanshi yaban tausayi
tahowata kawai nayi na barshi kinsanni da karfin
hali
Baraka ta bata rai kai yakamata a nemi mafita
Al-Ameen yayi kawata zan soki dashi don na
hango kun dace kwarai. Ta sata ta zabga tagumi
ta zuba mata ido, ina tsoron Abba Baraka bazan
iya dumfararsa da wann maganr ba bayan jiyan
nan yaja min kunne ya gaya min burinsa akaina
ina zansa raina nima inason Al-Ameen!
Ta dafe goshi ga koshi ga kwanan yunwa,
Baraka tayi iya tunaninta ta rasa mafita, sbd
tsoron hanyar da za'abi a dumfari Uban dwk don
haka ta numfasa tace to ai shikenan sai ku dauki
hakuri idan kuma yana iya dakatawa ya jiraki ko
kuwa? Tace kyaleni haushi ya isheni dauko wani
topic din kona manta da wann. Tayi yar dariya to
ya skul? Mu koma wancan fannin dame-dame
suka faru? Ta gyara zama suka tsinke da hirar
makaranta daga abinci sai sallah har zuwa bayan
la'asar lokacin da Mama ke niyyar tafiya da zarar
ta idar da sallah.Tana sallamewa yaro ya shigo
wai ana kiran Mama ta leko tace jeka kace ta
tafi Inna ta leko tace uwaki baki zuwa ko
wanene? Kai kace gata nan zuwa. Yaro ya fice
inna taci gaba da fada ba kyau wulakanci ko baki
son sa ki saurare shi ki bashi hakuri a zauan lfy,
ta shige daki Inna kenan bazaki gane ba. Ta
maida after dress dinta tasa mayafi tace Baraka
zoki rakani, donAllah ki tafi ke kadai kinsan sirrin
da zakuyi? Ta ja tsaki ta fito yana tsaye a kofar
gidan haba gimbiya, kuma saiki tafi kibarni da
tension? Ina kikeso nasa raina yau wllh ko abinci
na kasa ci sbd tunanin matsalar da kika ambato.
Tayi masa zuru tausayinsa ne zalla ke bin jinin
jinkinta tace kasan Allah nima tunani na ya kara
na rasa me zancewa Abba ganin yan'uwana ma
na jini ya dakatar dasu balle wani kuma watakila
kana bukatar auren ne da wuri kaga Abba bazai
amince ba. Ya goge zufar goshinsa da hankici,
don dai in jure ki karee sakandire zan iya jira
mana. Idan ma kinaso cigaba ne bayan munyi
aure ni zan dauki nauyin ki karanta duk fannin da
kikeso donAllah ki taimakeni kiyiwa Abba wann
bayanin. Ta dafe goshi! Wane zan masa ya gane?
Ya fada a ransa yace na dameki ko? Yes nima
nasan na fiye naci ga duk abnd nake so. Yace
mata tunda baki da abinyi ni ina dashi abnd nake
bukata daga gareki kawai ki tabbatar min
tsakaninki da Allah har cikin mind dinki kina
sona? Ki fada kanki tsaya kawai! Mamana tana
gab da fitowa zamu tafi.Tace Al-Ameen na
amince kar kaji wani shakku a ranka amma......
Ya dan daga mata hannu don't sai it pls! Kin
faranta min rai Sakeena na tabbata zan samu
inci abinci ya wuce min. Sauran magana ki kyale
min, nace yanzu me zaki bani na rike na
alkawari? Al-Ameen fa na bata mmk na yadda
gaba daya ya sallama kansa gareta ko shiyasa
itama ya mamaye mata ko ina? Tayi dan
murmushi me zan baka kuwa? Ya nuna yatsanta
wann ring din yayi min kyau shi zaki bani, ai
bazai yi maka ba, inji wa? Miko shinan ki gani.
Ba
musu ta zaro ta mika masa ya turawa karamin
yatsarsa zobe yayi zamansa daram kamar daman
can na sane.