Dan wasa daya ne ya rage wa Arsenal ta sayo ta iya cin kofunan Turai in ji Alisher Usmanov daya daga cikin mafiya yawan hannun jari a kulob din.
Mai tsaron raga Petr Cech ne kadai Arsene Wenger ya sayo zuwa Arsenal daga Chelsea a bana.
Kuma ana rade-radin cewar Karim Benzema na Real Madrid zai koma Arsenal kafin wasan Premier da za ta fara da West Ham ranar Lahadi.
A wata hira da CNN Usmanov, ya ce "In ban da wurin dan wasa daya, ina ganin Arsenal ta shirya cin kofunan Turai".
A ranar Lahadi Arsenal ta doke Chelsea a wasan Community Shield da ci daya mai ban haushi, kuma Alex Oxlade-Chamberlain ne ya ci kwallon.
Chelsea ake hasashen za ta kara lashe Premier bana, amma kuma Arsenal wacce ta kammala gasar bara a mataki na uku za ta kalubalanci daukar kofin.