Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid CF dake a Spain ta yarda da tayin da Arsenal FC tayi ma dan wasan nan dan asalin Faransa, Karim Benzema.
Wannan a cewar wani tsohon dan wasa ne kuma Koci, Rodney Marsh, cewa Gunners na shirin bada Fam Miliyan 48 domin sayen dan wasan mai shekaru 27, wanda Los Blanco ya amince.
“Na samu kira na waya daga abokina wanda yake a Real Madrid wanda ya sanar dani cewa Madrid ta yarda da cinikin da Arsenal tayi ma Benzema akan kudi Fam Miliyan 48.
“A baya, mutumin bai bata yin karya ba, amma dai mu tsaya mu gani. Da aka tambaye shi a shafin Twitter ko cinikin ya tabbata, A’a, tayi dai ne kawai.” Yace.