Jam’iyyar APC ta zabe gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El Rufai ya jagoranci kwamitin mutane 7 domin zaben didda gwani wanda za’ayi a Jihar Kogi.
Sauran mutanen dake cikin kwamiti din sune, Sanata Magnus Abbe wanda shine Sakatare, Alhaji Ibrahim Sarki, Misis Omorge Osifor, Mista Mohammad Wali, Mista Lanre Asiwaju da Mista Greg Egwu. Jaridar Leadership ta ruwaito.
An kafa kwamitin dai a jiya 26 ga watan Agusta a Ofis din APC na kasa.
A cewar Mataimakin Ciyaman na Arewa, Sanata Lawan Shu’iabu, an bi a hanakali wajen zaben mutanen dake cikin kwamitin din domin samun nasara.
A lokacin rantsar dasu, babban Sakataren shirye shirye na APC na kasa, Sanata Osita Izunaso ya bukaci su da su dauki aikin da aka basu da muhimmanci.