Rahotanni daga jihar Filato a Nigeria na cewa wasu 'yan bindiga masu muggan makamai sun yi wa kauyen Bisichi kawanya a karamar hukumar Barkin Ladi inda suka rika bude wuta.
Mazauna kauyen Bisichi sun wayi gari da jin karar harbe-harben bindiga daga sassa daban-daban na kauyen.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Filato, DSP Abuh Emmanuel, ya tabbatar da kawanyar amma ya ce an tura karin jami'an tsaro domin tabbatar da doka da oda.
Ya kara da cewar bai da cikakken bayanin hakikannin wadandan harin ya shafa.
Galibin mazauna yankin na Bisichi, Hausawa da Fulani ne kuma suna zargin 'yan kabilar Berom ne da kai masu hari, sai dai 'yan kabilar ta Berom sun musanta.
Title :
Ana zaman dar-dar a kauyen Barkin Ladi
Description : Rahotanni daga jihar Filato a Nigeria na cewa wasu 'yan bindiga masu muggan makamai sun yi wa kauyen Bisichi kawanya a karamar hukuma...
Rating :
5