Hukumomi a kasar Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane hudu ranar Laraba.
Uku daga cikin mutanen 'yan kasar ne da aka samu da laifin kisan kai; na hudu kuma dan kasar Syria ne da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu, an yanke hukuncin kisa a kan mutane 130, lamarin da ke nuna karuwar wadanda ake yankewa hukuncin kisan.
A ranar Talata, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta soki kasar ta Saudiyya a kan abin da ta kira "hanyoyin yanke hukuncinta masu cike da kura kurai", kana ta bukaci a dakatar da yanke hukuncin kisa.
Yawanci ana fille kan mutanen da aka samu da laifin kisan kai da fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi da kuma ridda ne a bainar jama'a.
Title :
An zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane a Saudiyya
Description : Hukumomi a kasar Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane hudu ranar Laraba. Uku daga cikin mutanen 'yan kasar ne da aka samu ...
Rating :
5