Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya isa Jamhuriyar Benin, inda ya samu gagarumar tarba.
Ziyarar wani bangare ne na ci gaba da tuntubar shugabannin kasashe makwabtan Najeriya dangane da yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suke fama da su.
matsalar tsaron da Nigeria ke fama da ita sakamakon rikicin Boko Haram, ta janyowa kasar koma baya ta fuskar tattalin arziki.
Kuma ziyarar ta zo ne a lokacin da Jumhuriyar Benin din ke bikin ranar Samun 'yancin-kai.