An gudanar da jana'izar babban basaraken kabilar Yarabawa, Ooni na Ife da ke Kudu maso yammacin Nigeria.
Sarakunan gargajiya da 'yan siyasa da manyan kasa sun taru domin cika tsarin al'adun kwana bakwai na binne gawar Oba Okunade Sijuwade, a birnin Ife.
Wannan sarkin shi ne sarkin kabilar Yarabawa, kabila ta biyu mafi yawan al'umma a cikin kabilun Nigeria.
An ce dubban mutane ne suka yi kwamba a birnin domin yin jana'izar wadda a shirya yi cikin kwanaki bakwai.
Ooni na Ifen tsatson Odudua ne, kuma bisa al'ada ba a cewa sarkin ya rasu, saidai a ce ya bi sahun kakanninsa.
An rufe bankuna da shaguna a garin, domin nuna alhini da karamci ga sarkin.
A watan Yuli ne sarkin, mai shekaru 85 ya rasu ne a wani asibiti a London, amma sai ranar Laraba da ta gabata ne aka fitar da sanarwar mutuwar.
An ce sarkin, wanda aka fi sani da Ooni na Ife, yana daga cikin zuri'ar ubangijin gargajiya na kabilar yarabawa watau Oduduwa.
Title :
An yi jana'izar Oba Sijiwade a Ife
Description : An gudanar da jana'izar babban basaraken kabilar Yarabawa, Ooni na Ife da ke Kudu maso yammacin Nigeria. Sarakunan gargajiya da 'ya...
Rating :
5