Wata kotu a kasar Masar ta yankewa jagoran jam'iyyar 'yan uwa musulmi Muhammad Badie hukuncin daurin rai-da-rai.
An yanke masa hukuncin tare da wasu masu fada aji na jam'iyyar 'yan uwa musulmi, bisa zargi da hannu a harin da aka kai caji ofis din 'yan sanda da ke Port Said a shekarar 2013.
Ana tuhumar Mr Badie da manyan laifuka da dama, inda wata kotun ta daban a Masar ta yanke masa hukuncin kisa a watan Afirilun da ya wuce.
Kuma ya na daga cikin dubban mambobin jam'iyyar 'yan uwa musulmi da aka garkame a gidan kaso, da tuhumar taimakawa gwagwarmayar da ta tabbatar da shugaba Mohammed Morsi darewa karagar mulkin kasar, kafin daga baya sojoji su yi juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatinsa.
Title :
An yankewa Mohammed Badie daurin rai-da-rai
Description : Wata kotu a kasar Masar ta yankewa jagoran jam'iyyar 'yan uwa musulmi Muhammad Badie hukuncin daurin rai-da-rai. An yanke masa huku...
Rating :
5