Sabon shugaban kamfanin man fetur na Nigeria, NNPC ya kori dukkan manyan daraktocin kamfanin.
Dr. Dr Emmanuel Ibe Kachikwu ya sallami manyan ma'aikatan kwana guda bayan da shugaba Buhari ya ba shi mukamin.
Bayanai sun ce, an maye gurbin manyan daraktoci takwas da aka sallama ne da wasu su hudu.
Kudaden harajin danyen ne ke samar wa Nigeria kashi 70 cikin 100 na kudaden shigarta amma a cikin 'yan shekarun nan batun cin hanci ne ya dabaibaiye harkar man.
Kwararru sun ba da shawarar a yi wa NNPC garan bawul domin toshe kofofin sama-da-fadi domin ciyar da Nigeria gaba.