Ana zargin wani matashi da ake zargin ya kware a kan harkar ta’addanci da kwacen kayan mutane da kuma sace-sace da kashe wani magidanci a kan Naira 100.
Shi dai wannan matashi mai suna Shehu Maijaki wanda dan asalin Jamhuriyyar Nijar ne ana zarginsa ne da kashe Murtala Haladu mai kimanin shekara 35 kuma dukkansu suna zaune ne a Layin Zomo da ke Falladan A karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya Jihar Kaduna.
Mahaifin marigayin mai suna Alhaji Haladu dankaka ya yi wa Aminiya bayanin yadda aka yi wa dansa Murtala Haladu kisan gilla a kan Naira 100, inda ya ce, “A ranar Asabar dana ya fita domin tafiya wurin kasuwancinsa a Kasuwar danmagaji, sai wani mai suna Shehu Maijaki ya bi shi a baya dauke da wani katon katako da aka kakkafa masa kusa ya buga masa a kansa kusoshin suka shige kansa suka makale inda hakan ya sa nan take ya fadi, kafin jama’a su kai masa dauki.”
Ya kara da cewa: “Nan da nan aka sanar da mu halin da yake ciki, mu kuma da isowa muka tallafe shi muka sa a cikin mota muka kai shi Asibitin St. Luks da ke Wusasa, inda bayan sun duba shi suka yi hoto na Naira dubu 30 daga bisani suka tura mu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, inda nan ma suka sa muka yi hoto na na Naira dubu 60. Kuma lamarin ya faru ne a ranar Asabar kuma ya rasu a ranar Larabar makon jiya da yamma.”
Da wakilinmu ya tambaye shi a kan me aka ce ya faru a tsakaninsu har ya haifar da hakasai ya ce, “To ni abin da na ji shi ne, akwai wani mai sayar da lemu a bakin hanya mai suna Bilya wanda yake auren kanwar Shehu Maijaki, shi ya ba marigayin Naira 100 don ya sayo masa tabar wiwi, shi kuma marigayi Murtala ya ce masa wannan wane irin wulakanci ne kake so ka min tunda ka san ba sana’ata ba ce kuma ka san ba na hulda da ita, don haka na rike Naira darin in ya so manya sa shiga tsakaninmu. Daga nan aka ce marigayin ya wuce.”
Malam Haladu ya ce sai shi mai sayar da lemu wato Bilya ya fada wa surukinsa Maijaki cewa dansa ya karbar masa Naira dari ya hana shi, kuma har da zagi don haka sai Maijakin ya sha alwashin daukar wa surukinsa fansa ta kowace hanya. “Wannan shi ne sanadiyyar kashe shi da ya yi domin an ce kwanansa biyu yana farautarsa. Kuma marigayin ya rasu ya bar matarsa da ciki da kuma ’ya’ya hudu. Don haka ina rokon hukuma ta dubi yadda ake yi wa jama’a kisan gilla ba tare da ana hukunta wadanda suke aikatawa ba, wannan yana janyo wa kasa masifa,” inji shi.
Wani mai suna Bello ya kara wa Aminiya bayani kan asalin fadan inda ya ce, “Na same su suna takaddama a kan Naira dari cewa dan Bilya Mai lemu na fama da bakon dauro sai wani ya ce masa idan ya dafa ganyen wiwi ya ba shi ya sha, kuma ya yi masa wanka, to, zai warke. Shi ne Bilya ya ba marigayin Naira dari ya sayo masa tabar wiwi, shi kuma marigayin ya rike kudin cewa an yi masa wulakanci tunda an san ba ya mu’amala da ita. Na sa hannu a aljihu na cire Naira dari biyu na mika musu domin in kashe wutar da ke tsakaninsu, washegari sai na ji an ce Maijaki ya caka wa marigayin kusoshi a kai.”
Da Aminiya ta tuntubi mahaifiyar Maijaki mai suna A’isha kasancewar mahaifin Maijaki, Malam Idris ya gudu ya boye saboda irin kalman da ake zargi ya yi na goyon bayan dansa a kan kisan, cewa ta yi “A gaskiya ban ji dadin abin da ya yi ba, kuma na yi bakin ciki sai dai ina roko su yafe mana, domin Allah ma ana yi maSa laifi Ya kuma yafe.
Dangane da gaskiyar cewa Maijaki ya kware wajen ta’addanci da daukar kayan jama’a kuma ana yi masa lakabi da Maijaki ne saboda ya taba sato jaki, sai ta ce, “To ka san jama’a idan wani abu ya faru irin wannan za ka rika jin bayanai daban-daban don haka sai dai mutum ya rika toshe kunne kawai.”
Rundunar ’Yan sandan Shiyya ta daya da ke Zariya ta tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda ta ce ta tura su ofishin bincike mai zurfi da ke Kaduna don bin bahasin lamarin.
Title :
An kashe magidanci a kan Naira 100
Description : Ana zargin wani matashi da ake zargin ya kware a kan harkar ta’addanci da kwacen kayan mutane da kuma sace-sace da kashe wani magidanci a ka...
Rating :
5