Jami'an tsaro a kasar Kamaru sun ce sun cafke wasu mutane uku da ake zargin 'yan Boko Haram ne da wasu ababan fashewa a birnin Maroua.
Biyu daga cikin wadannan mutane 'yan asalin Kamaru ne a yayin da kuma daya daga ciki shi dan Najeriya ne.
Ana zargin cewa wadannan mutane 'yan kungiyar Boko haram ne wadanda ke shirin sake kai wani hari na kunar bakin wake.
Akalla mutane 40 ne suka hallaka a kwanakin baya a birnin Maroua inda wasu 'yan tada kayar baya suka kai hari a wurare uku masu cunkoson jama'a