Babban birnin Afghanistan wato Kabul ya fuskanci jerin hare-haren bama-bamai wadanda suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla 40 tare da raunata wasu da dama.
Wani mutum sanye da kayan 'yan sanda ne ya tayar da bam a wajen kwalejin horo ta yan sanda lamarin da ya haddasa mutuwar mutane akalla ashirin da biyar.
Kazalika masu tayar da kayar baya sun kuma kai hari akan sansanin sojoji na kungiyar tsaro ta NATO wanda ke kusa da filin jirgin sama na kasar.
Sojan kasar Afghanistan tare da mahara biyu sun mutu sakamakon harin.
Haka kuma a safiyar jiya jumma'a bam ya tashi a cikin wata babbar mota a kusa da wani ginin gwamnati inda fararen hula 15 suka mutu.