Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty Internation ta yi Allawadai da hukuncin kisan da gwamnatin Chadi ta zartar ga wasu mutane 10'yan Boko Haram.
An samu mutanen 10 da hannu dumu-dumu a tagwayen hare-haren da aka kai babban birnin kasar Chadin Njamena a watan Yulin da ya wuce, wanda akalla mutane 8 suka rasa rayukansu.
An dai yi kwanaki uku ana gudanar da wanann shari'a, inda a ranar juma'a aka yankewa mutanen hukuncin kisa, a jiya asabar kuma aka zartar da shi ta hanyar bindige su.
Amnesty ta ce hukumomin Chadi sun yi abinda 'yan Boko Haram ke aikatawa, wato take hakkin bil'adama, kuma ba a bi ka'idojin da suka dace ba a shari'ar da aiwatar da hukuncin.
A bayyane take Chadi ta dauki wanann mataki ne, dan turawa da tsattsauran aike ga 'yan Boko Haram da masu taimaka musu, kan cewar duk wanda aka samu da laifi hukuncin kisa zai tabbata a gare shi a wata sabuwar doka da aka rattabawa hannu a kasar.
Title :
Amnesty ta yi Allawadai da hukuncin Chadi
Description : Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty Internation ta yi Allawadai da hukuncin kisan da gwamnatin Chadi ta zartar ga wasu mutane 10...
Rating :
5