Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce nan da wasu 'yan makonni za a soma shari'ar mutanen da suka sace dukiyar kasa.
A jawabinsa ga kwamitin zaman lafiya karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru domin magance matsalar cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da kuma rashin tsaro a kasar.
A cewarsa ba kawai zai sa a maido da kudaden da aka boye a bankunan kasashen waje ba kadai, saboda zai tabbatar da cewa wadanda suka yi satan sun fuskanci kuliya.
"Mun ci baya a cikin 'yan shekarun nan a matsayinmu na kasa, shi ya sa muke cikin matsalar tattalin arziki da kuma tsaro!" In ji Buhari.
A nasa bangaren, tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Janar AbdulSalami Abubakar ya bukaci shugaba Buhari ya tabbatar da bin doka da oda a kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa
Title :
An kusa soma shari'ar barayin gwamnati
Description : Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce nan da wasu 'yan makonni za a soma shari'ar mutanen da suka sace dukiyar kasa. A jawabinsa...
Rating :
5