Al'umma daga ko'ina a fadin Japan sun nuna alhininsu na 'yan dakikoki domin tunawa da shekaru 70 da kai wa birnin Hiroshima harin makami mai linzami na nukiliya.
A ranar 6 ga watan Ogustan shekarar 1945 ne wani jirgin yakin Amurka ya jefa makami mai linzami a birnin Hiroshima. Nan take kuma mutane dubu 70 suka mutu. Sannan daga bisani wasu dubu 70 din suka kara mutuwa sakamakon illar da tiririn gubar ya yi musu.
Kwanaki uku bayan nan Amurkar ta kara jefa wani bom mai guba a birnin Nagasaki.
An yi yakinin cewa wannan shi ne karon farko da aka yi amfani da makami mai guba akan bil'adama, a duniya.
Wannan ne yasanya Japan din mika wuya a lokacin yakin duniya na biyu.