Duk abinda bishira
zatayi kada
takulata. To ita duk bawannan
bne damuwarta ba, damuwarta
ynda Abba sam yaki nuna
sha'awarta gare shi, duk
dayasan tana sallah, hka nan
duk lokacin dakwananshi yajuyo
kanta sai dai ya jefa filo akan
kujera ya kwanta. Takasa gane
ma'anar hakan, tun tanajin
dadin ynda bai nemeta ba
saboda tsoronsa da take harta
dawo tasoma jin haushi. Ita ma
fa mutum ce cikakka mai lafiya,
sannan tana kwana daki daya
da san kacecen abun sonta ya
ya ba zata damu ba? Sai dai tayi
wa kanta alkawarin a yau in
zasu shekara ahaka ba za ta
taba yi masa tallar kanta ba
ma'ana baza takai masa kanta
ba. Sai dai zatayi masa kyale-
kyale taga karshen girman kai,
ta kosa su hadu da fati don ta
bata sakon kananan kaya tasiyo
mata don ta bata labarin cewa
ta kwashe su a wambai.
Kwananta goma taso ma girka,
duk tsawon kwanakin nan
abincin siyarwa dana umma
suke ci, domin bishira taki dafa
abinci. Ranar da zata fara girki
ta haukata gidan da kamshi,
tuwon shinkafa miyar shuwaka,
tasan Abba nason tuwon
shinkafa. Tun kafin ya dawo
yamata waya ta aika shagonshi,
'yan shago sun ci suna santi,
haka nan ya gayyaci abokansa
kofar gida ya shimfida musu
tabarma suka ci tare da lemu,
zobo da kunun aya. (reall ehem tazubo mun nawa na
koma 1 site ina kimtsa cikina
lolx) ga nama ya wadata a ciki,
abba yaji dadin yanda
abokanshi sukayi ta santi,
safiyar ranar kuma kunun gyada
ta musu da kosai. Duk wannan
abincin da ummi keyi bishira ko
a harshenta ta ki ci, cewa ma
tayi ita fa kowa tayi girkinta don
baza ta ci abincin ummi ba.
Kuma ba shegiyar dazatai wa
girki, hakan yayi wa ummi dadi
don nata ganin ta bakin
tsohuwa ce, da ta ce ko kwai
bishira tadafa shine dai dai a
cikin bawo to baza ta iya ci ba
bare wani abinci. Sun zauna
tsawon wata daya ahaka ummi
bata taba leka ko kofar gida ba,
tana kewar ummanta gara ma
tsohuwa duk ranar juma'a in
tadawo masallaci takan biyo
gidan taga takwararta. Dakinta
Abba yake yagama karyawa ya
shirya zai tafi aiki, ummi ta kalle
shi tana son tambayar zuwa
gidan umma tna jin tsoro. Ya
dubeta kamar kina son cewa
wani abu ko? Ta ce am dama
inaso inje gida in gaida su
umma, yajuyo yadubeta suka
hada ido. Gabanta yafadi, ta
sunkuyar dakanta, yace a'a
tadaga ido takalle shi, wani
kunci taji aranta, ga matanshi
nan yini take garari a layi bata
ko tambaya amma ita ta
tambaya shine ma zai hanata?
Ya dauki jakar shi, ta mike ta
rakashi har tsaka gida tare da yi
masa addu'ar Allah yatsare, yini
tayi da takaici dama haka mata
suke ji in an hana su zuwa
anguwa? Daran ranar zai koma
ga bishira don haka bata san
dawowarshi, tana kwance kan
doguwar kujera tana karanta
littafin hausa ( naleka muku
kozanga sunan littafin amma
bangano mukuba) kamshin
turaren shi ne yasa tasan
yashigo, don littafin yadauki
hankalinta. Ta amsa sallamar
daya sake yi tare da mikewa
zaune, yana sanye da kananan
kaya tamkar wani dan saurayi,
yayi kyau a idonta kamar ta
rungumeshi. Tace sannu
dazuwa yace yawwa, dauko
mayafinki muje tazura takalma
bayan tagoge sannan ta ciro
mayafi, yace a'a dauko hijabin.
Ta maida ta dauko hijabi tafito
sannan yakulle kofar, saida suka
fita waje sannan yadubeta,
hannu rabbana zakije musu?
Tace yaya Abba toni bani da
kudi ai. Sukabi ta wani super
market suka sai sabulai da
turare, akafa suke takawa sannu
ahankali suka jero duk da cewa
bawata hira suke ba, Abba ne
yake amsa waya jifa-jifa na
jama'a masu sonshi. Tun daga
nesa suka hangi mahaifansu
suna cin abinci a inda suka
saba. Alhaji babba dakarami.
Cikin zumudi ummi ta ce, yauwa
gasu alh. Abba yaje haka zakije
musu da rawar kanki ko? Cikin
shagwaba tace, wanne rawar
kai nayi toni yaya Abba? Yace, na
gani kinayi kamar zaki kwasa da
gudu, kafin tayi magana sun iso
gurin dukkansu suka zube akan
tabarmar daga gefe. Abba ne
yasoma cewa, sannunku alh. Alh.
Yace, a'a kune? Alh karami yace,
uwata harda ke? Tace, eh ina
yininku? Sukace lpy lau. Alh.
Karami yace, uwata kunanan lpy
ba wta matsala ko? Ta ce, ba
komai alh.. Yace to Allah yyi
maku albarka, ya azurtaku da
'ya'ya ma su albarka wadanda
kuma zasu biku. Abba yace amin
suka hada baki da Alhaji babba,
alh babba yaci gaba da cewa,
Abba ya hakurin shirmen ummi
kuma? Ince dai bawata matsala?
Abba yakalleta mun gode Allah
alh, amma bwata matsala, ummi
tamike dazumudi bari a karasa.
Tun daga soro take kwala ma
umma kira. Umma tce, A'a
muryar wa nake ji haka? Ummi
tashigo da gudu ta cakume
umma, tsohuwa tafito tana
fadin lale. Dakin tsohuwa
tasoma shiga suka gaisa sannan
tadawo dakin umma, sun gaisa
umma tasake mata nasiha,
ummi tace umma ni matsalata
daya matarsa. Kullum saitayi min
habaici tana zagina wata rana r
harda kawayenta