Ya aje kular kofar dakin ummi
yaleka dakin bishira, tana
kwance kan gado, itafa bata jin
cewa zata dazama dakishiya,
dole cikin biyu ayi daya, kota
tada ballin dazai saketa komuma
tanemi duk wata hanyar daza
akori wannan 'yar iskar
yarinyar. Yashiga dakin,
muhibba daketa wasa akan
gadon da baya zaton tun da aka
kafashi tasake kakkabe shi, yace
hibba. Yarinyar ta waiwayo cikin
murna tanufo ubanta da dan
gwaranci, bishira tasa hannu
tasuri 'yarta yace, bishira duk
wannan abin daki keyi
fabashine mafita agare kiba. Ki
kwantar da hankalinki ki nutsu
ki kama girmanki, yarinyar nan
zata biki amma in kin zabi
akasin haka kece zaki koko.... Kai
malam! Ta katse shi, bafa wata
sauran magana fanasan komai,
ni yanzun saki kurum nafi
muradi, ya ce sakin lafiya? Ni
yanzun ma na soma sonki,
tadaga mishi hannu tare da
daga murya, nikuma nadaina
sonka, karya ne makace kana
sona kuma kanason waccan
banzar. Dole acikinmu akwai
wadda kafi so. Abba yace to ai
kece, ke nafi son kuma ita tasan
haka, kalmar tashi tadan
sanyaya mata zuciya. Don haka
bata sake magana ba, yace kina
bukatar wani abu ne? Tace don
Allah nidai ka fita kawai, yace to
na fita. Ummi lokacin tana canza
kaya zuwa riga dazani na leshi,
sosai tayi kwalliya tamkar
kasureta ka ruga don kyau.
Fuskarta sake ta tari Abbanta
dasannu dazuwa, ita ce tasa
musu abinci kowa da plate
dinshi, amma sai ya aje nashi
yace suci nata. Dama taso yin
hakan amma tana tsoron kada
ya gwasaleta, sai da sukayi dam
sannan yace bari yayi wanka
tatashi takai masa ruwan wanka
tadawo. Kafin ya fito ta sake
gyara ko ina, jallabiya mai
gajeran hannu yasaka mara
nauyi ya wadata jikinshi da
turaruka tana kallonshi cikin
sha'awa. Taso taimaka mishi tun
agurin shafa mai, amma tana
tsoron kada yaga zakewarta,
don haka tashare tare da cewa
dasannu za azo gurin. Ysake
cewa zai koma shago, tace haba
yaya Abba yanzun kuma?
Yadauko tape dinshi nagwada
mutane, zo in gwadaki, har da
kayanki zan yaka yanzun.
Yarannan 'yan shiriritane, badon
naje dazun ba dasun sani
nasaba alkawari, dinkunan su
kawai suka yi tayi suka aje
wanda nabasu. Ummi tabata
fuska, ya tausasa murya, come
on zo in gwada ki, bazan jima
bakinji ko? Tatashi taje
gabanshi ta tsaya. Sai dai
mamakinta duk dunkunan da Ya
Abba ya sha yi mata abaya bai
taba gwadata basai yanzun?
Koya manta yanda yake mata
ne? Tsawon siket din ta ya soma
gwadawa, tana tunani sai taji
ratsawar dan yatsansa tare da
tape din a kwankwasonta, duk
da cewa dariga ajikinta saida
hakan yasa taji wani yanayi
ajikinta. Har ma takalle shi, haka
nan ya auna hips dinta da
kirjinta, shi kanshi ya shiga wani
yanayi alokacin, haka nan
yakoma shagon cike dakewarta.
Kayan bacci tasaka ta kwanta a
gadon tana da yakinin bazai
mata komai ba, tunda yasan
bata sallah. Har kusan goma da
rabi tana jiran shigo warshi
shiru, waya tadauka ta rubuta
mishi sako da cewa. Ya abba
don Allah kadawo ni dai tsoro
nake ji. Ya karanta yayi
murmushi, azuciyarshi yace, don
ita ya kwafe, yayi dunkunan
yana son kudin don ya sai mata
akwati da kayan shafa zuwa
kayan ciki. Share ta yayi sai
kusan sha daya darabi sannan
yatashi tare da sallamar yaran,
haka nan itama sai daya hado
mata duguwa rigarta ta shadda
wadda dama anriga anyi sirfani
ajikinta. Dakin bishira yasoma
lekawa, bacci yadauketa sosai
agefen gadon take da alamun
baccin yazo mata ba cikin shiri
ba. Abba yayi murmushi tare da
cewa, wa ya fada miki ana cin
bashin bacci? Ina zaton matar
nan jiya bata runtsa ba, yau
gashi yazo ba shiri. Har ya gyara
mata kwanciya itama 'yar ya
gyara ta amma bishira bata
farka ba, don haka yakashe
mata wuta yafita. Yaso kashe
injin amma garin da zafi gashi
basu kawo wutar nepa ba,
gidan yarufe yazo ya tura kofar
ummi data rufe. Karar kofar ne
ya farkar da ita amma bata
motsa ba, tun daga kofar
yatsaya yana kallonta, can
tsakiyar gadon takwanta bata
dora kanta saman filo ba. Amma
tana manne da filo daya
akirjinta fuskarta yake kallo, a
jikinta taji kallonta yakeyi. Kusan
minti 4 sannan ya aje ledar
hannunshi. Shirin bacci yake
amma yakasa daina kollonta,
shikanshi yana mamakin
wannar jarababben son dayake
ma ummi, duk da dakewar
dayake don kada yabada kanshi
amma sai yadinga jin wani abu
yana fisgarshi. Tamkar yafito
mata da zallan sonshi gareta,
tsoronshi inta gano kila
tarainashi. Kadan-kadan takan
bude ido ta saci kallonshi, sai
daya gama komai a tunanin ta
ya kwanta a gadon amma sai
taga yadauki filo yakwanta a
kan kujera. Haka suka rayu har
tsawon sati daya, ranar yabar
dakin ummi ranar kuma tasoma
salla, ita ko bishira satin nan tayi
shine tamkar mahaukaciya
sabon kamu. Ranar kuma da
abba yadawo dakinta bata
runtsa ba shima bata barshi ya
runtsa ba, daga bisani dole
yabar dakin yakoma falonta
yakwanta. Haka gidan yaci gaba
da kasancewa, in Abba yafita
ummi bata da sauran sakewa
saboda zagi da habaicin bishira.
Wani sa'in har da kawayenta, ko
makota 'yan jam'iyarta su shigo
suyi tayi, ummi bata kula su.