Majalisar dattawan Najeriya ta zartar da wani kudiri na tura tawaga ta musamman wadanda zasu ziyarci yankin arewa maso gabashin kasar wanda ayyukan Boko Haram suka nakasa.
Ana saran 'yan tawagar karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawan, Sanata Bukola Saraki za su ziyarci yankin ne domin su ganewa idanuwansu halin da yake ciki.
Abubuwan da za su duba dai sun hada da irin girman barnar da hare-haren Boko Haram suka yi wa yankin da yanayin da al'ummar suke ciki sannan kuma su saurari koke-kokensu.
Tawagar za ta kuma mayar da hankali kan yanayi da halin da jami'an tsaro suke ciki a yankin.
Haka kuma Majalisar ta dattawa ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa wani kwamiti da zai yi aikin farfado da yankin da kuma sake dawo da mutanen yankin na arewa maso gabashin Najeriya gidajensu.