Shugaban Amurka Barack Obama ya kama hanyarsa ta zuwa Kenya a ziyararsa ta farko a matsayin shugaban kasa zuwa kasar mahaifinsa.
Mr Obama ya shaida wa manema labarai cewa wannan ziyara ta nuna jajircewar Amurka game da yaki da ta'addanci a gabashin Afirka.
Shugaban ya kuma dauki alkawarin yin magana ta keke-da-keke a kan cin hanci da take hakkokin bil adama a Kenya.
Zai kuma kare fafutukar da yake yi a kan 'yancin da 'yan luwadi suke da shi a kasar da ake musguna musu.
Ana tsammanin Mr Obama zai gana da 'yanuwansa a babban birnin kasar Nairobi, amma ba zai je kauyen da aka haifi mahaifinsa ba.
Shi ne kuma zai kasance shugaban Kasar Amurka na farko da zai yi jawabi ga Taron Kungiyar Kasashen Afirka idan ya je kasar Habasha a ranar Lahadi.