Wani saurayi ne ya je wajen ma'aikin Allah ya ce, ya ma'aikin Allah kai min izini na yi zina, sai mutane suka hayyako masa suna cewa, tir da kai!
Sai ma'aikin Allah ya ce masa ya matso kusa da shi, sai ya matso ya zauna. Da ga nan sai ma'aikin Allah ya ce masa, za ka so ma mahaifiyarka yin zina? Sai ya ce, 'a'a Wallahi, Allah sanyani fansarka! Sai ma'aikin Allah ya ce, hakanan mutane ba za su so ma mahaifiyarsu yin zina ba. Sai ma'aikin Allah ya ce masa, za ka so ma 'yarka zina? Sai ya ce, 'a'a Wallahi, Allah ya sa ni fansarka! Sai ma'aikin Allah ya ce, hakanan mutane ba za su so ma 'yarsu zina ba. Sai ma'aikin Allah ya ce masa, za ka so ma kanwarka zina? Sai ya ce, 'a'a Wallahi, Allah sanyani fansarka. Sai ma'aikin Allah ya ce, haka nan mutane ba za su so ma kanwarsu zina ba. Sai ma'aikin Allah ya ce, za ka so ma goggonka zina? Sai ya ce, 'a'a Wallahi, Allah sanyani fansarka! Sai ma'aikin Allah ya ce, hakanan mutane ba za su so ma goggonsu zina ba. Sai ya sake ce masa, za ka so ma innarka zina? Sai ya ce, 'a'a Wallahi, Allah sanyani fansarka! Sai ma'akin Allah ya ce, hakanan mutane ba za su so ma innarsu zina ba.
------------------------------------------
Daga nan Sai Manzon Allah ya yi masa addu'a ya ce: "Ya Allah ka gafarta masa zunubinsa, ka tsarkake zuciyarsa, ka kuma katange masa farjinsa".
---------------------------
Ahmad ya ruwaito shi Albani kuma ya kawo shi cikin Sahiha.