Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi taka tsantsan game da batun cire tallafin man fetur saboda kada ya jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.
Wata sanarwa da babban mai taimaka masa a harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu ya aikewa manema labarai, ta ce Shugaba Buhari ya karbi shawarwari daban-daban kan dalilan da suka sanya ake so ya cire tallafin man, yana mai cewa akasarin shawarwarin ba su da inganci.
A cewar sa, "Idan aka kara farashin man fetur, hakan zai sa a samu karuwar farashin sufuri da kayan abinci da kudin haya na mutanen da ke karbar albashi. Haka kuma akwai mutane da dama da ba su da ayyukan yi, kuma su ma lamarin zai shafe su."
Shugaba Buhari ya bayyana wannan matsayi ne lokacin da manyan jami'an ma'aikatar man fetur suka ziyarce shi domin yi masa bayani kan halin da bangaren albarkatun man fetur na kasar ke ciki.
Shugaban na Najeriya ya ce yin zagon-kasa da fasa bututun mai da cin hanci da rashawa da kuma almubazzaranci ne suka addabi ma'aikatar man fetur, ba wai batun bayar da tallafi man ba.
A baya dai batun cire tallafin man fetur a Najeriya yana cikin manyan batutuwan da 'yan kasar ke mayar da hankalinsu a kai, inda akasarin su suke adawa da shi, suna masu cewa ko da gwamnati ta cire ba za a yi amfani da kudin domin inganta rayuwar su ba.