Akalla mutane uku ne suka rasa ransu,wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon Turmutsutsu da aka yi yayin karbar zakka, a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Bayanai dai sun ce Jama'a da dama da suka hada da nakasassu da mutanen gari ne suka hallara yayin da ake raba zakkar, a gidan wani mai hannu da shuni a jihar.
An ce mutumin ya saba bayar da zakkar duk shekara kuma a na wanyewa lafiya sabanin ta bana.
Wasu sun alakanta dalilin mutuwar mutanen da sanya ranar karbar zakkar ta zamo daya ga maza da mata abin da ya kawo turmutsutsu, sabanin a baya a inda a kan sanya ranakun karbar zakkar daban-daban ga jinsin guda biyu.
Yanzu dai hukumomi sun dakatar da mai hannu da shunin da raba zakkar har sai an ga yiwuwar ci gaba da ita.