Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya fadi cewa gwamnatinsa ba za ta kore yiwuwar tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram ba dangane da sakin 'yan matan sakandare na Chibok sama da 200 da kungiyar ta yi garkuwa da su tun watan Aprilun shekarar 2014.
Shugaba Buharin ya fadi hakan ne a yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na CNN, jiya Talata, a kasar Amurka, a ci gaba da ziyarar kwanaki hudu da ya ke yi a kasar.
Sai dai kuma shugaban ya ce dole ne gwamnatinsa ta yi takatsantsan wajen sahihancin aniyar shugabannin kungiyar kan tattaunawar.
Sannan kuma ya ce sai an tabbatar da su waye jagororinta na hakika domin mutane da dama suna fitowa su yi ikrarin jagorancin kungiyar.
Dangane kuma da batun yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Buharin ya ce ba bu wani mutum da zai zama shafaffe da mai domin kasancewarsa dan wata jam'iyya ko kuma yana jin shi wani ne.